1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shria'ar Amirka da kamfanin Google

October 22, 2020

An fara shari'ar da gwamnatin Amirka ta shigar da kamfanin Google, wanda ke zama mafi girma wajen neman bayanai a kafar Intanet, bisa zargin kamfanin yana dakile hanyoyin samun gasa.

https://p.dw.com/p/3kI0a
Google-Logo
Hoto: picture alliance / Geisler-Fotopress

Wannan matsalar dai ta karu musamman ta wayoyin salula. Kamfanin yana kashe makuden biliyoyin kudi a shekarun da suka gabata ga masu kera wayoyin na salula. Burin shi ne saka manhajar Google a wayoyin hannun. Wannan ya janyo matukar wahala ga masu neman gasa da kamfanin na Google su iya wani tasiri. Hakan ya sa gwamnatin Amirka ta dauki matakin shari'a, kamar yadda mataimakin mai gabatar da kara na kasar ta Amirka Jeff Rosen ya yi karin haske yana mai cewa: "Idan gwamnatin Amirka ba ta yi amfani da dokokin hana tarnaki ga gogayyar kasuwanci ba, za mu shiga cikin kasadar rasa masu kirkira nan gaba. Mutanen Amirka za su iya rasa wani kamfanin kamar Google."

Shi dai kamfanin na Google yana ganin shari'ar cike take da kuskure da tababa. Babu wanda ya tilasta wa mutane amfanin da shafin tambaya na Google, kamar yadda kamfanin ya bayyana yayin taron manema labarai. Sai dai kawai yana samar da abu mafi inganci da mutane ke bukata. Game da saka manhajar a wayoyin hannu, kamfanin ya kwatanta kansa da sauran abubuwan da mutane ke amfani da su yau da kullum.
Sai dai Gabriel Weinberg shugaban manhaja na shafin neman bayanai da ake kira Duck Duck Go da ke gogayya da Google, na da ra'ayi na daban, inda ya ce babu sauki wajen sauya wa daga Google zuwa sauran shafukan kamar yadda kamfanin Google ke ikirari, abin da ya janyo har yanzu suka gaza wuce samun fiye da kaso biyu cikin 100 a kasuwar neman bayanan ta intanet. Wani abu kan wannan shari'ar shi ne duk jam'iyyun siyasa na Amirka guda biyu Democrats da Republicans suna goyon bayan matakin. Amma kowa yana da nasa dalilin.

App Icons Facebook Whatsapp Snapchat Google Youtube Spotify
Facebook da Whatsapp da Snapchat da Google da Youtube da SpotifyHoto: picture-alliance/dpa/V. Wolf

'Yan Republican sun yi imanin Google na yada manufofin 'yan gaba-dai gaba-dai da boye ra'ayin 'yan mazan jiya. Bincike mai zaman kansa bai tabbatar da wannan ikirari ba. Shair'ar za ta nuna irin tasirin siyasar Amirka ga manyan kamfanonin fasaha da suka hada da Google da Facebook da Amazon da Apple da suke karawa 'yan siyasa karfi. Yanzu abin tambaya dai shi ne, yadda za a wanye da kamfanin na Google. Ana iya kwashe shekaru ana takun sakar, kamar yadda aka yi da kamfanin Microsoft a shekarun 1990.