Shari'ar tshohon shugaban Chadi
July 20, 2015Shi dai Hissene Habré ya na sanye da farar tufafin nan nasa na al'ada lokacin da jami'an tsaro suka tasa keyarsa cikin kotu ta musamman a birnin Dakar. Dalili kuwa shi ne ya bayyana cewar ba zai gurfana ba gaban kuliya saboda bai amince da ita ba, alhali shugabannin kasashen Afirka ne suka kafata domin sauraran shari'ar kisan kare dangi da ake zarginsa da aikatawa a lokacin da yake rike da madafun ikon kasar Chadi.
Hissene Habré dai shi ne tsohon shugaban wata kasa ta Afirka na farko da ake yi wa shari'a a gaban kotun da wannan nahiya ta kafa. Saboda haka ne shari'ar ke shiga cikin kanun labaru, musamman ma a Senegal inda ya samu mafaka. Hasali ma dai a Dakar babban birnin wannan kasa ne aka kama Habre, shekaru 23 bayan da aka hambarar da gwamnatinsa sakamakon juyin mulki a shekarar 1990.
Farfesa Demba Mbow ta ce wannan ta zama wani abin alfahiri ga kasashen nahiyar Afirka musamman Senegal, kasncewar ita ce ta yi uwa da makarbiya a harkokin da suka shafi Habré.
"Ya fi dacewa Senegal ta gudanar ta shari'ar maimakon wata kasa saboda ana sa ran cewar alkalai zasu yi adalci, lamarin da zai bayar da damar karfafa wanke kaurin suna da Afrika ta yi tare da inganta harkarta ta shari'a."
Alkalai uku ne dai suke sauraran wannan shari'a ta Hissene Habré biyu 'yan Senegal yayin da babban alkali ya fito daga wata kasa ta daban ta nahiyar Afirka. Tun da farko dai masu shigar da kara hudu sun shafe shekara guda da rabi suna gudanar da bincike a Chadi kan zargin da ake yi wa tsohon shugaban wannan kasa na aikata ta'asa da kuma kisan gilla a zamanin mulkinsa. Baya ga tono kaburbura na bai daya, masu shigar da kara sun yi nazarin jerin takardun da hukumar leken asirin ta tsohon shugaban na Chadi ta mika musu.
Sai dai kuma duk kokarin da fannin shari'a ya yi don jin ta bakin Hissene habré dangane da laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa ya ci tura saboda ya ki cewa uffan. Ko da a lokacin da ya hallara ba da son ransa ba gaban kotu a wannan Litinin, ba abin da Hissene Habré ya ce illa tofin Allah tsine dangane da abin da ya danganta da mulkin mallaka. Amma kuma Angélique Savane da ke zama masaniyar halayyar dan Adam, shari'ar Habré na iya zama babban darasi ga shugabannin Afirka da ke neman gudanar da mulkin kama karya.
"Wai shin wannan shari'a ta Hissene Habré za ta iya magance wadannan tarin matsalolin? E za su share wasu laifukan da ya aikata tun da zukatan dangi wadanda ya kashe ko ciwa zarafi za su sanyi. Amma kuma ba zai magance mulkin kama karya da wasu shugabannin ke gudanarwa a Afirka ba, saboda suna gadaran canja kundin tsarin mulki don ci gaba da mulki. A takaice ma dai suna gudanar da salon mulki ne na sai Mahdi ka ture."
Hissene Habré ya mulki Chadi ne na tsawon shekaru takwas wato tsakanin 1982 zuwa 1990. Amma kuma bayan da shugaban Chadi na yanzu Idriss Deby Itno ya hambarar da gwamnatinsa ya yi hijira zuwa kasar Senagal, inda ake yi masa shari'a. Fiye da 'yan kasarsa 4000 ne suka shigar da kara bisa zargin Hissene Habré da musguna musu ko kuma cin zarafin wani danginsu lokacin da ya ke rike da madafun iko. Kotun ta musamman ta rigaya ta sanar da cewar sama da shaidu 100 za su bayar da bahasi dangane da zargin kisan kare dangi da ake yi wa Hissen Habré.