1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara taron murkushe cutar murar tsuntsaye a Senegal

February 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7D

Shugaban kasar Senegal Abdoullahi Wade ya bukaci kasashen nahiyar Africa dasu dauki ingantattun matakai na rigakafi don murkushe cutar murar tsuntsaye, da a yanzu kewa duniya baraza.

Shugaban na Senegal wanda ya fadi hakan a lokacin bude wani taron wuni biyu na kasashe 15 na nahiyar Africa, dake cikin kungiyyar Ecowas a can birnin Dakar a yau laraba , ya kuma bukaci da kasashen su samar da cibiyar nazari a game da wannan cuta a nahiyar.

Shirya wannan taro dai a cewar bayanai ya biyo bayan bullar cutar ne mai nau´in H5N1 a nahiyar ta Africa a can tarayyar Nigeria.

Mahalarta taron da suka fito daga cikin kasashen 15, da kuma kasar Mauritania, an tabbatar da cewa ya kuma sami halartar wakilan hukumar lafiya ta duniya da kuma ta kula da harkokin gona ta Mdd.