Sudan: Masu zanga-zanga sun gamu da fushin 'yan sanda
June 30, 2019Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne a wasu unguwanni na Bari, al-Mamoura da Arkaweit, da ke wajen birnin Khartum inda dubban masu zanga-zangar da suka fito suka yi dandazo. Wasu rahotanni daga gabashin kasar ta Sudan musamman a Gadaref, sun ce a can din ma 'yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye kan masu zanga-zangar tare da tarwatsasu.
Jami'an tsaron kasar ta Sudan sun jibge askarawan rundunar RSF kan motoci da makamai a ko'ina cikin birnin a wani mataki na shirin ko ta kwana. Wannan al'amarin na zuwa ne duk da kiraye-kiranyen kwantar da tarzoma da kiyaye hakin masu zanga-zanga da hukumomin kare hakin dan Adam na kasa da kasa suka yiw a gwamnatin rikon kwarya ta kasar Sudan, duba da yadda aka samu kisan jama'a masu bore da adawa da gwamnatin mulkin soja a farkon wannan wata.