1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawarwakin matasan Isra'ila da suka ɓace a yammacin Kogin Jordan

June 30, 2014

Kafofin yada labarun Isra'ila sun ce jami'ai sun tabbatar cewa gawarwakin na daliban ne su uku da ake nema tun a ranar 12 ga watan Yuni.

https://p.dw.com/p/1CT10
Leichen von vermissten israelischen Jugendlichen gefunden
Hoto: picture-alliance/dpa

Dakarun tsaron Isra'ila sun gano gawarwakin matasan nan uku da suka ɓace a gabar yammacin Kogin Jordan a farkon watan Yuni. Kafofin yaɗa labarun Isra'ila sun rawaito jami'an ƙasar na tabbatar cewa gawarwakin na daliban ne su uku da ake nema tun a ranar 12 ga watan Yuni. Yanzu haka dai majalisar ministoci Isra'ila ta kira wani zaman gaggawa da yammacin wannan rana ta Litinin don tattauna irin matakan da za ta ɗauka. Isra'ila dai ta zargi Ƙungiyar Hamas da ke iko a Zirin Gaza da hannu wajen sace matasan. Sai dai Hamas ba ta tabbatar ko ƙaryata wannan zargi ba. Ƙasar ta Yahudun Isra'ila dai ta tura dakaru cikin yankunan gaɓar yammacin Kogin Jordan don neman matasan 'yan shekarun haihuwa daga 16 zuwa 19.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahamane Hassane