Kasa cimma yarjejeniyar mulki a Sudan
May 21, 2019Talla
Sojojin kasar Sudan da suka jagoranci kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir na fuskantar matsin lamba daga kasashen waje kan mika mulki ga farar hula, abinda ke zama babban burin masu zanga-zangar.
Bangarorin biyu sun sha shiga tattaunawa don kafa sabon kwamiti da zai ja ragamar mulkin kasar na tsawon shekaru uku kafin gudanar da zabe, kungiyoyin farar hula na fatan samun rinjaye a cikin mabobin kwamitin mulkin. Ana sa rai bangarorin biyu za su sake komawa teburin tattaunawa domin samun mafita kan rikicin da kasar ke ciki.