1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gwabza kazamin fada tsakanin ´yan Taliban da sojojin gwamnati

April 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1y

´Yan tawayen Taliban 41 da kuma ´yan sanda 6 aka kashe a wani mummunan fada da aka gwabza a kudancin Afghanistan a wani yanki inda shugaban taliban ya taba zama. An kwashe tsawon ranar jiya ana gwabza fadan a kudu maso yammacin birnin Kandahar. Jiragen yakin soji Amirka sun yi ta harba makamai masu linzami don marawa dakarun Afghanistan dake yaki da ´yan tawaye a kasa. Gwamnan birnin Kandahar Assadullah Khalid ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa an halaka ´yan Taliban 41 sannan an jiwa da dama rauni. Sannan ´yan sanda shi da sun bakwanci lahira yayin da 9 suka samu raunuka. A halin da ake ciki an kame ´yan Taliban 13.