1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojojin NATO uku a Afganistan

Gazali Abdou Tasawa
August 5, 2018

Sojojin rundunar tsaron kasa da kasa ta NATO guda uku sun mutu a cikin wani harin kunar bakin wake da aka kai wa ayarin motocinsu a Afganistan.

https://p.dw.com/p/32eAZ
Afghanistan US-Soldaten in der Provinz Logar
Hoto: Reuters/O. Sobhani

A Afganistan sojoji uku na rundunar tsaron kasa da kasa ta NATO sun halaka, wasu uku da suka hada da na Amirka daya sun jikkata a wannan Lahadi, cikin wani harin kunar bakin wake da aka kai a kan ayarin motocinsu na sintiri a kusa da garin Charikar na jihar Parwan mai nisan kilomita kimanin 70 da birnin Kabul. 

Rundunar RS wato Resolute Support ta sojojin NATO a Afganistan ta tabbatar da afkuwar harin wanda ta ce an kai shi ne da misalin karfe shida na safiyar wannan lahadi, sai dai kuma ba ta bayyana asalin kasashen sujojin uku da suka mutu ba a cikin harin. 

Tuni dai Kungiyar Taliban ta dauki alhakin kai wannan hari a shafinta na Tweeter inda ta ce ta halaka da kuma jikkata a jimulce sojojin takwas na kasar Amirka da ta kira sojojin mamaya.