1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An halaka wasu Isra'ilawa da wuka a Kudus

May 6, 2022

Akalla mutum uku ne rahotanni ke cewa wasu mahara dauke da wukake suka kashe a gabashin birnin Tel Aviv na kasar Isra'ila. Harin ya zo ne yayin da ake bikin 'yancin kai.

https://p.dw.com/p/4Atxw
Israel Messerangriff in Elad
Hoto: Ahmad Gharabli/AFP/Getty Images

Maharan da ba a san ko su wanene ba sun yi amfani ne da wuka a kan jama'a a wani gari da aka kira Elad, inda wasu mutum biyar ma ke cikin mawuyacin hali.

Babu dai wani karin haske game da tushen wadanda suka kai harin wanda ya zo yayin da Isra'ila ke bikinta na samun 'yancin kai  a jiya Alhamis.

Falasdinawa da dama na bayyana bikin a matsayin wani bala'i, kasancewar sama da mutum dubu 700 ne suka tsere wa kasar a shekara ta 1948 lokacin da ta ayyana samun 'yancin kan.

Tun a karshen watan Maris ne dai ake ta samun hare-hare a Isra'ila, abin kuma da ya haddasa asarar rayukan akalla mutum 15.