1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka wani kusa na al-Qaida a Libiya

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2018

Ma'aikatar tsaron Amirka ta tabbatar da mutuwar Moussa Abou Daoud wani kusa na Kungiyar al-Qaida a kasar Libiya a cikin wani harin sama da aka kai a ranar 24 ga wannan watan na Maris.

https://p.dw.com/p/2v9iZ
USA Bomben Symbolbild
Hoto: M. Ammons/picture-alliance/USAF

Ma'aikatar tsaron Amirka ta tabbatar da mutuwar wani kusa na Kungiyar al-Qaida a kasar Libiya. A cikin wata sanarwa da babban kwamandan rindunar sojin Amirka a Afirka ta Africom ya fitar a wannan laraba, ya bayyana cewa sun hallaka Moussa Abou Daoud daya daga cikin shugabannin Kungiyar  Aqmi da wani na hannun daman sa a lokacin wasu hare-hare ta sama da suka kaddamar tare da hadin gwiwar sojojin halasttaciyar gwamnatin Libiya ta Fayez al-Sarraj a ranar 24 ga wannan watan na Maris a kusa da garin Oubari na Kudancin kasar ta Libiya. 

Amirka dai ta bayyana Moussa Abou Daoud a matsayin mutuman da ke horas da sabbin dauka na Kungiyar ta Aqmi kan yadda za su iya kai hare-haren ta'addanci a yankin, kana ya taimaka wa Kungiyar ta Aqmi da kayan aiki da kudi da kuma makamai domin harar duk wasu kadarorin Amirka da na kasashen Turai a yankin.