Hukumar 'yan sandan Najeriya ta haramta rundunar musamman
October 4, 2020Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya sanar da haramta jami'an rundunar musamman da ke yaki da ‘yan fashi da makami ta kasar daga zuwa sintiri da saka shinge bincike idan har ba suna sanye da kayan aiki na ‘yan sanda ba.
A sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriyar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Frank Mba ya sanya hannu ya ce daga yanzu dole ne ‘yan sandan su sanya kayan aikinsu ba kawai su rinka fita sintiri a kayna gida ba.
Wannan ya biyo bayan zargin kashe wani matashi da ‘yan sandan rundunar ta SARS suka yi a Lagos inda suka bi matashi n har otel dinsa suka harbe shi tare da tafiya da motarsa.
Rundunar ‘yan sanda ta sanar da kame mutanen da ake zargi da aikata laifin a Lagos. To sai dai ba wannan ne karon farko da ‘yan sandan suke sanar da wannan haramci ba. Masu fafutukar kare hakin jama'a na kiran a yiwa rundunar garambawul ko kuma a rusata gaba daya.