1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rusa tsohuwar jam'iyya mai mulkin Sudan

Suleiman Babayo USU
November 29, 2019

Hukumomin kasar Sudan sun haramta tsohuwar jam'iyyar mai mulki kasar ta tsohon Shugaba Omar Hassan al-Bashir wanda ya shafe kimanin shekaru 30 kan madafun iko lamarin da ya janyo dafifin masu tsallen murna.

https://p.dw.com/p/3TvHO
Sudan Proteste in Khartum
Hoto: Reuters/M. N. Abdallah

Hukumomin kasar Sudan sun haramta tsohuwar jam'iyyar mai mulki kasar ta tsohon Shugaba Omar Hassan al-Bashir lamarin da ya janyo dafifin masu tsallen murna a birnin Khartoum fadar gwamnati. Tsohon Shugaban Bashir da jam'iyyarsa ta National Congress Party (NCP) sun mulki kasar na kimanin shekaru 30 tun daga shekarar 1989 lokacin da ya kwace madafun iko ta hanyar juyin mulki.

A watan Afrilu na wannan shekara masu zanga-zanga suka kawo karshen gwamnatin ta al-Bashir, kuma Firaminista Abdalla Hamdok na kasar ta Sudan ya jagoranci zaman majalisar zartaswar da aka rushe tsohuwar jam'iyyar mai mulkin kasar ta Sudan.