1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ji amon harbe-harbe a Khartoum

Binta Aliyu Zurmi
April 26, 2023

An shiga rana ta biyu a yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Sojojin gwamnati da dakarun sa kai na rundunar RSF a kasar Sudan.

https://p.dw.com/p/4QYyO
Sudan | Kämpfe in Khartoum
Hoto: AFP/Getty Images

To sai dai an ji amon harbe-harbe da shawagin jiragen yaki gami da tashin bama-bamai a birnin Khartoum a cewar jakada na musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Volker Perthes, a yayin wata gamnawa da ya yi da kwamitin tsaro na Majalisar.

Perthes ya bayyana cewar yana ci gaba da tattaunawa da bangarorin sojojin da ke fada da juna, a cewarsa babu wata alama da ke nuna suna da muradin hawa teburin tattaunawa.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, WHO ta yi gragadi a kan amfani da muggan sinadarai masu guba bayan da sojojin da ke fada da juna suka mamaye dakunan gwaje-gwajen kimiyya.

Ya zuwa yanzu, wannan rikici ya halaka rayukan mutane sama da 450 yayin da ya jikkata wasu dubbai.