1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da dokar ta-baci kan Ebola

August 8, 2014

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta kaddamar da dokar ta-baci a kan cutar Ebola da ta addabi yankin yammacin Afirka.

https://p.dw.com/p/1CrGP
Hoto: Reuters

Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO ta kuma sanya cutar ta Ebola a matsayin cutar da ke neman daukar matakan gaggauwa domin shawo kanta a matakin kasa da kasa domin dakile yaduwarta da kuma shawo kanta. Dama dai tuni kasashen yammacin Afirka suka kaddamar da dokar ta-baci kan cutar ta Ebola mai saurin kisa da ta addabi kasashen yankin domin dakile yaduwarta zuwa sassan da cutar ba ta bulla ba. Dakarun sojoji a Laberiya sun sanya shingaye a kan titunan gundumar Cape Mount inda annobar cutar ta Ebola ta fi kamari domin takaita zirga-zirgar mutane zuwa Monrovia babban birnin kasar.

A kasar Saliyo hukumomin kasar sun kafa dokar ta-baci domin dakile yaduwar cutar ta Ebola. Kiyasin Hukumar Lafiya ta Duniya ya nunar da cewa ta lakume rayuka sama da 930 wasu sama da 1,700 suka kamu da ita tun bayan barkewar annobar a yankin yammacin Afirka. Kawo yanzu Hukumar Lafiya ta Duniyar ba ta dauki matakin hana zirga-zirga a tsakanin kasashen da suke fama da annobar cutar Ebolan ba.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo