1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kaddamar da hare-haren kan mayakan IS a Siriya da Iraki

Muntaqa AhiwaApril 5, 2015

Sojojin hadin gwiwa sun kaddamar da sabbin hare-hare ta sama a kan mayakan IS dake a kasashen Siriya da Iraki.

https://p.dw.com/p/1F2zZ
Luftangriffe der USA gegen IS
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Nickel

Hare-haren da suka kaddamar dasu cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an kai guda 12 ne a sansanonin mayakan IS din ne da ke a Masoul na kasar Iraki.

Sabbin hare-haren na zuwa ne yayin da ake kwashe mutane 2000 akasari, falasdinawa, daga sansanin ‘yan hijira na Yarmuk dake Damascus na kasar Syria, bayan karbe kusan ilahirin yankin da mayakan IS suka yi.

Kamar yadda wani jami'an wata kungiyar Falasdinawa, Anwar Abdul Hadi ya fada a yau, an kwashi mutanen 2000 ne tsakanin ranar Juma'a da jiya Asabar, inda aka bi dasu ta wasu hanyoyin da ke da tsaron sojin da suka hana mayakan na IS wuce yankin dake cikin lardin Zahira.