1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar hana zirga-zirga a Damaturu

Usman ShehuOctober 25, 2013

Hukumomi a jihar Yobe sun kafa dokar hana fita ba dare ba rana a Damaturu, babban birnin jihar bayan wani sabon tashin hankali da ya barke.

https://p.dw.com/p/1A5zS
Soldiers stand during a parade in Baga village on the outskirts of Maiduguri, in the north-eastern state of Borno May 13, 2013. To match Insight NIGERIA-ISLAMISTS-INSIGHT/ REUTERS/Tim Cocks (NIGERIA - Tags: MILITARY CIVIL UNREST)
Sojojin da aka tura su yaki Boko HaramHoto: Reuters

Rahotanni daga garin Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yobe, sun tabbatar da cewa an dauki tsawon lokaci ana ba-ta-kashi tsakanin wasu ‘yan bindiga. Rikicin dai ana kyautata zaton ya faru ne tsakanin ‘yan kungiyar Boko Haram da jami'an tsaro, bayan wasu hare-hare da ‘yan bindigar suka kai a sassan garin. Al'ummomin da ke zaune a anguwar Red Bricks da ke kan hanyar Maiduguri da ma masu makobtaka da su sun bayyana cewa an dauki lokaci ana jin kararraki a yankin. Wani bawan Allah da ke zaune a wannan wuri ya shaida wa wakilinmu Al-Amin Sulaiman Muhammed ta wayar tarho, bisa sharadin boye sunansa cewa.

"Ya ce tun da misalin karfe biyar da wasu mintuna ne muka fara jin karan harbe-harbe a anguwa da ake kira Red Brick da ke kan hanyar Maiduguri a gaskiya wannan lamari ya tayar mana da hankali saboda mun fi shekara ba mu ji karar irin wannan harbi ba. A halin yanzu da muke wannan maganar ma wannan harbe-harben ana yin sa"


Mawallafi: Al-Amin Sulaiman Muhammed

Edita: Usman Shehu Usman