1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar ta-baci a Libiya

September 2, 2018

Hukumomi sun ayyana dokar ta-baci a birnin Tripolin kasar Libiya saboda fitintinu cikin makon da ya gabata.

https://p.dw.com/p/34Bxj
Libyen Tripolis Kämpfe zwischen Milizen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Mahukunta a kasar Libiya sun ayyana dokar ta-baci a birnin Tripoli da kewaye bayan tashin hankalin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 39 cikin makon da ya gabata.

Gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ce ta kafa dokar a wannan Lahadi.

Hukumomin sun ce an yi hakan ne domin dakile yaduwar rigimar da ta barke tsakanin bangarorin da ke hamaiya da juna da kuma masu goyon bayan gwamnati kan ikon mallakar wasu yankuna.

Wasu mayakan tawaye ne dai ke tayar da kayar baya dangane da batun ikon wasu muhimman yankuna na kasar.

Libiya dai ta shiga rudani ne bayan kisan Shugaba Moamar Ghadafi a shekarar 2011.