1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hare-haren Bam a Najeriya

February 1, 2018

Wasu hare-haren kunar bakin wake kan wani sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar ya yi sanadiyar asarar rayuka da ma jikkatar wasu a wajen birnin Maiduguri.

https://p.dw.com/p/2rsqx
Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Rahotannin da ke fitowa daga Najeriya, na cewa an kai wasu hare-haren kunar bakin wake kan wani sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Kamar dai yadda jami'an agaji suka tabbatar, harin farko ya faru ne da yammacin ranar Laraba a wajen birnin Maiduguri inda akalla aka rasa rayukan mutane hudu tare da jikkatar wasu sama da 40. Bayan wasu 'yan mintoci ne kuma wata yarinya ta tayar da Bam dinta a wani sashe na hada-hada a sansanin, sai dai babu wani wanda da ya mutu ko ya jikkata.

Hare-haren dai na zuwa ne yayin da dakarun Najeriya ke fatattakar mayakan Boko Haram a babbar maboyarsu ta sansanin Sambisa.