An kai hari a birnin Kabul
April 20, 2019Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Kabul babban birnin Afghanistan, na cewa ana can ana ta musayar wuta tsakanin dakarun kasar da wasu 'yan bindiga, bayan kaddamar da harin bom da ranar yau.
Maharan sun fara ne da tayar da bom a kwaryar birnin na Kabul, kafin kuma daga bisani suka nufi ma'aikatar sadarwa, a cewar Ministan harkokin cikin gida Nasrat Rahimi.
Bayanan da ke fitowa na cewa an halaka wasu daga cikin maharan.
Hayaki kuwa ya turnike babban ginin ma'aikatar da wata matattarar bayanai, wadanda duk ba su da nisa da fadar shugaban kasa.
Ba a san 'yan bindigar da suka kai harin ba, kamar yadda yake a bangaren wadanda suka salwanta.
Kungiyar Taliban ta yi barazanar kai wa cibiyoyin gwamnati hare-hare, koda yake ba ta dauki alhakin harin ba.