An kai hari a gaban fadar sarkin Saudiyya
October 8, 2017Talla
Rahotanni daga kasar Saudiyya na cewa a jiya Asabar wani mutum dauke da bindiga ya kai hari tare da halaka jami'an tsaro biyu a fadar sarkin Saudiyyar a birnin Jeddah, wasu mutanen uku kuma suka jikkata.
Kamfanin dillancin labaran kasar ta Saudiyya SPA ya ruwaito ministan cikin gida na kasar na cewa maharin ya kai farmakin ne dauke da bindiga kirar Kalashnikov da gurneti guda uku inda ya bude wuta tun a bakin kofar fadar tare da kashe biyu daga cikin askarawan da ke gadi, kafin daga karshe a yi nasarar bindige shi.