An kai hari kan 'yar jaridar DW a Kenya
May 1, 2021Talla
An kai wa wata 'yar Jarida mai aiko wa tashar Deutsche Welle rahotanni hari da hayaki mai hawaye yayin da ta ke daukar rahotanni wani taron gangami a Nairobi babban birnin kasar Kenya a wannan rana ta asabar.
'Yar Jaridar Mariel Mueller tare da mai Kamara dake daukar mata hoton bidiyo ta ce an harba musu konson hayaki mai sa hawaye yayin da suke nadar hira da daya daga cikin masu zanga zangar.
Masu zanga zangar dai na adawa ne da yadda 'yan sanda ke cin zarafin al'umma da kuma rashin ayyukan yi saboda annobar Corona.
Tuni tashar Deutsche Welle ta yi Allah wadai da harin. Ita ma kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta soki harin ta kuma bukaci a gudanar da bincike.