An kai harin bam kan ayarin NATO
August 4, 2017Talla
Rahotanni daga Kabul babban birnin kasar Afghanistan, sun ce an kai harin kunar bakin wake a kan ayarin motocin jami'an kungiyar tsaro ta NATO, inda aka halaka soja daya wasu kuwa sukaa jikkata. Lamarin ya faru ne a gundumar Qarabah, inda wani jami'in sojin da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce sojan da ya mutun ba na Amirka ba ne, kamar yadda wasu ruwayoyi suka nunar.
Bayanai sun ce ana can ana kulawa da wadanda suka jikkatan a asibitin sojin Amirka da ke harabar runudunar soji da ke Bagram. Babu dai wani cikakken labari kan ko alkaluman wadanda za su mutu ka iya karuwa.