1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wani harin bama-bamai a Afghanistan

August 30, 2014

'Yan kungiyar Taliban sun kai hari ga wani ofishin jami'an asirin kasar da ke a birnin Jalalabad a yankin gabacin kasar, tare kuma da harbe-harbe.

https://p.dw.com/p/1D3yn
Afghanistan Taliban verüben Anschlag auf Gebäude des Geheimdienstes in Dschalalabad 30.08.2014
Hoto: Reuters

A cewar Ahmad Zia Abdulzaï, mai magana da yawun gwamnan wannan yanki, harin dai ya wakana ne ta hanyar amfani da wata mota mai dauke da bama-bamai da ta tarwatse, inda hakan yayi sanadiyar mutuwar a kalla mutane uku a cewar ma'aikatan ofishin dake jihar Nangarhar.

Sai dai kuma daga nashi bengare Darectan babban Asibitin birnin na Nangarhar Dr Najeebullah Kamawal ya sanar cewa, sun samu a kalla mutane shidda da suka rasu, yayin da wasu 46 suka jikkata sakamakon harin, inda a halin yanzu 26 daga cikin su ke kwance a Asibitin. Daga nasu bengare 'yan kungiyar ta Taliban ta bakin kakakin su Zabihullah Mujahid sun dauki alhakin kai wannan hari tare da tabbatar da samun mace-mace da dama.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Souleiman Babayo