SiyasaJamus
An kai wani sabon harin rokoki a Kabul
August 30, 2021Talla
Fadar White House ta Amirka ta tabbatar da harin da aka kai a wurin da aka kira Salim Karwan. An kuma ji karar harbe-harbe lokacin da rokokin ke sauka.
A gefe gudu kuwa harin nan da Amirka ta kai a kan kusoshin mayakan IS a Afghanistan a ranar Lahadi, ya yi sanadiyyar wasu fararen hula.
Sojojin Amirka da suka tabbatar da hakan, sun ce daga cikin wadanda abin ya shafa dai har da wasu kananan yara hudu a kusa da filin jirgin saman na Kabul.
Shaidu ma sun ce mutane shida suka mutu a harin na jiya da Amirka ta yi amfani da jirgi marar matuki, yayin da karin mutane da yawa suka kuma jikkata.