An kama Alexei Navalny bayan ya koma gida
January 17, 2021Talla
Tun da farko mahukuntan kasar sun karkata akalar jirgin da ke dauke da Mr. Navalnya ya zuwa filin jirgin saman Sheremetyevo, sabanin filin jirgin saman Vnukova inda ya shirya sauka bayan da ya tashi daga Berlin. Magoya bayansa da 'yan jarida dai sun yi ta dakon saukarsa Vnukova kamar yadda wani dan jarida na kamafnin dillancin labarai na AFP da ke cikin jirgin ya sanar.
Gabanin fitar wannan sanarwa dai jami'an 'yan sanda sun kame da dama daga cikin magoya Navaly din kana suka tarwatsa dandazon mutanen da ke jiran isowarsa.
Dama tun kafin wannan rana mahukuntan na Rasha ke barazanar za su kama shi idan ya shiga kasar bayan da kotu ta bukaci ya gurfana a gabanta.