An kama wani ɗan Ƙungiyar IS a Moroko
January 18, 2016Talla
Mutumin wanda aka kama a garin Al Mohammadiya kusa a gidan mahaifiyrasa .
Bincike jami'an tsaro ya nuna cewar ya je Siriya tare da ɗaya daga cikin 'yan ƙunar baƙin waken na Paris inda ya samu horo daga Ƙungiyar Al-Nosra kafin daga baya ya shiga Ƙungiyar IS. Hukumomin tsaron na Moroko sun daɗe suna gudanar da bincike a kan mutumin wanda yake yawan zuwa ƙasar kai a kai.Mutane kusan 130 suka mutu a hare-haren na Paris waɗanda aka kai a ckin watan Nuwamba da ya gabata