1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: An tsare 'yan gidan sarauta

Abdul-raheem Hassan
March 7, 2020

Wasu 'yan gidan sarautar Saudiyya sun shiga hannun hukumomin kasar bayan bankado shirin kifar da mulkin Sarki Salman da dansa Yerima Mohammed bin Salman mai jiran gado.

https://p.dw.com/p/3Z16v
Kronprinz von Saudi-Arabien Mohammad bin Salman
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/S. Walsh

Mujjalar Wall Street Journal ta ce a ranar Juma'a dogarai na kotun masarautar Saudiyya suka kai samame gidan 'dan uwan sarki Salman Yerima Ahmed bin Abdulaziz a Saud, da kuma tsohon yarima Mohammed bin Nayef, wanda sarki Salman ya tube a 2017 ya nada dansa.

Babu wani martani kan wannan mataki daga masarautar Saudiyya ko hukumomin kasar zuwa yanzu.