1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron muhalli a Cancun

December 11, 2010

Taron muhalli na duniya ya ɗauki ƙudirin taimakawa ƙasashe matalauta shawo kan sauyin yanayi

https://p.dw.com/p/QWAo
Hoto: DW/Jeppesen

Taron ƙasashen duniya kan sauyin muhalli wanda aka kammala jiya a birnin Cancun na ƙasar Mexico ya cimma ƙudirori da suka haɗa da kafa sabon asusu na musamman domin taimakawa ƙasashe matalauta shawo kan sauyin yanayin da kuma rage hayaƙi mai guba na masana'antu.

A bana dai taron ya taka rawar gani saɓanin ruɗanin da ya fuskanta a taron da ya gudana a Kopenhagen a bara. Ƙasashe kimanin 190 waɗanda suka hallara a Mexico basu yarda sun ɗauki dogon buri ba inda suka maida hankali kawai kan samun mafita ga muhimman batutuwan kare sauyin muhallin wanda a ƙarshe suka amince a ci-gaba da aiwatar da yarjejeniyar Kyoto tare da samar da asusun kuɗi ƙarƙashin hukumar gudanarwa mai mutane 24 da za ta haɗa da wakilan ƙasashe masu tasowa da kuma manyan ƙasashe masu ci-gaban domin taimakawa ƙasashe matalauta shawo kan matsalolin sauyin muhallin.

Dukkanin ƙasashen sun kasance cikin farin ciki da murna tare da jinjinawa sakatariyar harkokin wajen Mexico, ƙasar da ta karɓi baƙuncin taron bisa gagarumar nasarar da taron ya cimma wanda ke zama masalaha ga sassan ƙasashen.

Sai dai kuma duk da adawar da shugaban tawagar ƙasar Boliviya Pablo Salon ya nuna cewa yin masalaha ya saɓa da tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya wadda ta buƙaci sai ɗaukacin ƙasashe sun kaɗa ƙuri'ar amincewa sannan yarjejeniyar za ta zama kammalalliya a hukumance. Sakatariyar harkokin wajen Mexico Patricia Espinosa wacce ta jagoranci tattaunawar ta kammala da jawabi tana mai cewa.

"Akwai dama ta buɗe sabon babi tare da yin la'akari da ci-gaban tattalin arziki da rage talauci da kuma kula da yanayin muhalli, mun yi karɓi hanzarin ka, mun kuma shigar da shi a saboda haka an amince da ƙudirin."

Daga nan ne ɗaukacin wakilan suka kwashe da tafi da miƙewa tsaye domin yi mata jinjina.

Yarjejeniyar da aka cimma ta amince da taimakawa ƙasashe matalauta kare dazukansu da yaƙi da sare itatuwa. Musamman dai ƙasashen Brazil da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo da kuma Indonesiya za su amfana daga wannan tsari.

A halin da ake ciki kuma tuni shugabanni suka fara maida martani tare da yabo ga yarjejeniyar da aka cimma. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya yi bayani yana mai cewa.

"Wannan taro ya nuna ana iya samun daidaiton ra'ayi tsakanin ƙasashen da suka ci-gaba da ƙasashe masu tasowa".

Wakilin kasar Amirka Todd Stem ya ce jadawalin da aka cimma ba su warware matsolin sauyin muhalli ba, amma dai matakin ci-gaba ne. Ita ma dai ƙasar Sin ta ce matakin abin a yaba ne.

Ministoci da dama na baiyana cewa babban ƙalubalen dake gaba, shine taron da za'a gudanar shekara mai zuwa a ƙasar Afirka ta Kudu inda za'a cimma muhimman yarjeniyoyi da suka shafi kare muhallin.

Ƙungiyar Tarayyar Turai da Japan da Amirka sun yi alƙawarin bada gudunmawar dala biliyan 30 ga asusun da aka buɗe na tallafawa ƙasashe matalauta da kuma dala miliyan dubu ɗari da za'a aiwatar nan da shekara ta 2020.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Mohammad Nasiru Awal