An kashe mai zanga-zanga daya a Sudan
October 25, 2022An bada rahoton kashe wani mai zanga-zanga daya a boren zagayowar ranar juyin mulkin Sudan, amma ba a san yawan mutane da suka jikkata ba. Sai dai hukumomin sun toshe yanar gizo tare da amfani da borkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zanga.
Bayanai sun nunar da cewa masu zanga-zangar sun kafa shingaye don hana jami'an tsaro tinkararsu yayin da sojoji suka toshe gadoji da hanyoyin domin hana su zuwa fadar shugaban kasa. A rana mai kamar ta yau a Shekara guda da ta gabata ne, Janar Abdel Fattah al-Burhane ya saba alkawuran da ya yi shekaru biyu da suka gabata, lamarin da ya dada jefa Sudan cikin mawuyacin halin tattalin arziki.
Masu zanga-zanga 119 ne suka mutu a cikin shekara guda sakamakon fafutkar da suka yi wajen neman tabbatar da dimokuradiyya a Sudan.