1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mayaƙan Ƙungiyar IS 18 a Libiya

Gazali Abdou TasawaJune 10, 2015

Mayaƙan na IS sun mutu ne a cikin wani faɗa da ya haɗasu da mayaƙan Ƙungiyar Majlis al- Choura ta wasu masu kishin islama a Ƙasar ta Libiya.

https://p.dw.com/p/1Ff5w
Libyen Kämpfe bei Sirte
Hoto: picture-alliance/dpa/Str

A Libiya a wannan Laraba mayaƘan ƙungiyar 'yan jihadi ta IS 18 sun hallaka a cikin wani ƙazamin faɗan da ya haɗasu da mayaƙan wata ƙungiya ta masu kishin islama a garin Derna da ke a gabascin ƙasar ta libiya.

Wasu shaidun gani da ido da ke a garin na Derna sun ruwaito cewa faɗan ya ɓarke ne a marecen Talata bayan mutuwar Salem Derbi shugaban Ƙungiyar Majlis al-Choura ta masu kishin islama na asar ta Libiya wanda mayaan IS suka kasheshi bayan da ya i ya yi mubayi'a ga jagoran Ƙungiyar IS Abu bakr al Bagdadi.