Sudan: Rikicin kabilanci ya barke
June 7, 2022Talla
Masu aiko da rahotanni sun ce rikicin ya fara barkewa ne a tsakanin kabilar Larabawa da wata kabilar kan filin noma a gudumar Kolbus mai tazarar kilo mita 160 daga yammacin Darfur inda aka kashe 16, kana daga bisani wani batakashi a yankin Abou Jebeiha tsakanin 'yan kabilar Kenana da na al-Hawazma ya hallaka mutane 11 tare da raunata wasu 35. Manzo na musamman na Majalisar Dinin Duniya a Sudan Volker Perthes, ya yi tir da Allah wadarai da harin, ya kuma bukaci da bangarorin da basa jituwa da su saka wa zukatansu ruwan sanyi, ya kuma yi kira da a kafa wani kwamitin na masu shiga tsakani don kawo karshen rikicin kabilancin da ke halakka fararen hula.