An kashe mutum a zanga-zagar Sudan
February 14, 2022Talla
Dubban jama'a dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce yin AlLah wadai da gwamnatin soji a karkashin jagorancin janar Abdel Fatah Al-Burhane sun fantsama a kan titunan birnin Khartum da wasu sauran garuruwan, domin tilasta wa gwamnatin mulkin sojin yin marabus. 'Yan sanda sun rika harbin masu yin gangami da barkono tsohuwa da kuma hayaki mai sa kwala. Wannan mutumin da aka harben shi ne cikon na 80 wanda da ya mutu tun lokacin da aka soma yin boren a cikin watan Oktoban da ya gabata.