An kashe wani babban komandan Taliban
August 30, 2007Talla
Maaimakar tsaro ta kasar Afghanistan tayi ikrarin kashe wani babban komandan kungiyar Taliban a kudancin kasar.Maaikatar ta fadi cikin wata sanarwa cewa dakarun sojin Afghanistan sunkashe Mullah Brodar a safiyar yau din cikin wani hari da suka kai a lardin Helmand.Mullah Brodar dai an baiyana cewa memba ne na majalisar shugabannin Taliban kuma wani babban komandan soji ne a yammacin Afghanistan a lokacin mulkin Taliban a kasar.Yana kuma da alaka ta kut da kut da shugaban kungiyar Mullah Omar.