1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe wani dan jarida a Sudan ta Kudu

Salissou BoukariAugust 20, 2015

Wasu mutane sun buda wuta kan wani dan jarida na kasar Sudan ta Kudu a Juba babban birnin kasar a yammacin ranar Laraba, bayan da ya bar ma'aikatarsa zuwa gida.

https://p.dw.com/p/1GIMN
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva KiirHoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Dan jaridar dai mai suna Peter Moi, na aiki ne da jaridar New Nation inda abokan aikinsa ke ganin cewa wannan kisa abu ne da aka shirya shi. Kisan dan jaridar ya biyo bayan wasu kalammai da shugaban kasar ta Sudan ta Kudu Salva Kiir ya yi, inda karara a bainar jama'a ya bayyana cewa zai kashe duk wani dan jarida da ke sukar muradun kasar, yana mai firtawa a gaban 'yan jaridar cewa, "incin 'yan jarida ba wai yana nufin zaku rinka sukar kasarku ba". Shugaban ya yi wadannan kalammai ne a filin jirgin saman kasar na birnin Juba yayin da yake shirin zuwa taron da ya gudana a birnin Addis Abeba na kasar Habasha. Kawo yanzu dai Ofishin 'yan sandar kasar bai ce uffan ba kan wannan kisa.