1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun kashe mai zanga-zanga a Sudan

Abdoulaye Mamane Amadou
March 24, 2022

Jami'an tsaro a Sudan kashe wani matashi mai shekaru 28 da ke tsaka da zanga-zanga bayan da suka harbe shi da harashen roba a yankin Madani mai tazarar kilo mita 200 daga birnin Karthum.

https://p.dw.com/p/490P3
Sudan | Proteste in Khartum
Hoto: AFP/Getty Images

Maatshin shi ne na 90 da a yanzu da suka mutu, tun bayan barkewar zanga-zangar kin jinin juyin mulkin da Janar Abdel Fattah al-Burhane ya yi, ga gwamnatin farar hula karkashin jagorancin Abdallah Hamdok a cikin watan Oktoban bara.

Daruruwan masu zanga-zanga sun sake fitowa a wannan Alhamis a yankuna da dama na kasar, da zummar nuna rashin jin dadi kan karin farashin kayayakin masarufi.

Ita dai Sudan da ke yankin gabashin Afirka, ta kasa samun firaminista da zai fito daga wani bangare na farar hula, tun bayan da Abdallah Hamdok ya jefar da kwallon mangwaro a farkon wannan shakara, bisa kasa cimma matsaya da sojojin da suka hambareshi a shekarar bara.