An kashe wasu jami'an Hukumar PAM
April 15, 2017Talla
Mutanen sun gamu da ajalinsu ne a kan hanyarsu ta zuwa wajen wani rumbun tsimi na hukumar inda suke yin aikin rarraba abinci. A sa'ilin da wani fadan da aka gwabza a garin Wau da ke a yankin arewa maso gabashin kasar tsakanin dakarun da ke yin biyayya ga shugaba Salva Kiir da kuma na tsohon mataimakinsa Riek Mashar ya rutsa da su. Ma'aikatan na PAM wadanda dukkaninisu guda uku 'yan Sudan ta Kudu ne, biyu an datsesu da ada, yayin da daya aka harbeshi har lahira.