Zaben Isra'ila karkashin matakan coronavirus
December 23, 2020Masu zabe a Isra'ila za su sake komawa runfunar kada kuri'a karo na hudu cikin kasa da shekaru biyu, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu yake shirin fuskantar tuhuma kan cin hanci, zargin da ya musanta.
Zaben wanda aka tsara a watan Maris na sabuwar shekara ta 2021, za a gudanar saboda rashin cimma matsaya kan kasafin kudi a majhalisar dokoki a wannan Talata da ta gabata duk da matakan da ake dauka na hana yaduwar annobar cutar coronavirus, lamarin da ya zama sabon kalubale ga Firamnista Benjamin Netanyahu wanda ya fi kowa dadewa kan mukamun tun da aka kafa Isra'ila, inda jam'iyyarsa ta Likud ke rike da madafun iko tun shekara ta 2009, lokacin da ya sake dawowa karagar mulki.
Shi dai Netanyahu dan shekaru 71 da haihuwa ya fara rike mukamun daga shekarar 1996 zuwa shekarar 1999.