An koma kai wa juna hare-hare a Sudan
June 22, 2023Talla
Mazuana birnin Khartoum sun ce ana ta musayar wuta tsakanin dakarun gwamnati da bangaren mayakan da ke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasa Mohammad Hamdan Daglo, a Khartoum din da kuma yankin Omdurman.
Haka ma akwai rahotannin wani fada a Dilling da ke a kudancin Kordofan, yankin mai tazarar wasu daruruwan kilomitoci da fadar gwamnatin kasar.
A farkon wannan makon ne dai aka tsagaita wutar domin ba da damar kai agajin jinkai a yankunan da ke matukar bukatar taimako.
Sama da mutum dubu biyu dai sun salwanta a Sudan, wasu sama da miliyan biyu da dubu 200 kuma sun tsere daga kasar tun bayan barkewar sabon yaki a ranar 15 ga watan Afrilu.