Sudan: An koma tebirin sulhu
July 4, 2019Talla
Tattaunawar ta yanzu da tawagogin bangarorin biyu ke yi na gudana ne a wani hotel na birnin na Khartoum kusa da gabar kogin Nilu a gaban mai shiga tsakani na kasar Habasha da na kungiyar tarayyar Afirka.
Bayan da suka share awoyi biyu suna tattaunawa cikin tsanaki a jiya Laraba, inda suka cimma matsaya kan sako dukkan fursinonin siyasa da ake tsare da su, bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tattaunawar tasu a wanann Alhamis.
Wannan dai shi ne karo na farko da bangarorin biyu suka sake zama tun bayan da sojojin kasar suka tarwatsa zaman dirshen na masu neman sauyin a gaban harabar hedikwatar sojojin kasar da ke a birnin Khartoum a farkon watan Yunin da ya gabata inda gwamman mutane suka rasa rayikansu.