Sabuwar tattaunawa da sojojin Sudan
May 14, 2019Talla
A Talatar nan ce aka sake komawa kan teburin tattaunawa tsakanin jagororin mulkin Sojin kasar Sudan da na bangaren masu zanga-zangar, domin ganin an maida mulki hannun farar hula, biyo-bayan barkewar wani sabon rikici a daren jiya Litinin da ya yi sanadiyyar hallaka mutum shida ciki har da jami'in tsaro guda.
Masu zanga-zangar dai sun taka gagarumar rawar da ta kawo karshen mulkin kama-karya na shekaru 30 na Al-Bashir, sai dai bayan sojoji sun hambarar da shi sai suka zama 'yan kama-wuri-zauna, lamarin da ya fusata matasan sake fantsama kan titunan kasar suna kiraye-kirayen mika mulkin hannun farar hula.
Amurka dai ta zargi rundunar Sojin kasar da hannu wajen harin na jiya da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum shida.