1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kori kwamandojin sojin Iraqi saboda gazawa

Mohammad Nasiru AwalNovember 13, 2014

Firaministan Iraqi Haider al-Abadi ya kori manyan kwamandojin sojin kasar sun 26 saboda laifin cin hanci da rashawa da kuma sakaci ga aiki.

https://p.dw.com/p/1Dmdm
Haider Abadi
Hoto: AFP/Getty Images

A wani kokarin sake inganta aikin sojojinsa a yakin da suke yi da nayakan kungiyar IS, Firaministan Iraqi Haider al-Abadi ya kori manyan kwamandojin sojin kasar sun 26 saboda laifin cin hanci da rashawa da kuma sakaci ga aiki. Abadi wanda ya sallami kwamandojin a ranar Laraba bai yi karin haske ba sannan ba a samu jami'a a ofishinsa domin karin bayani game da kwamandojin da wannan mataki ya shafa ba. Sai dai a wani jawabi da aka watsa ta gidan telebijin Firaminista Abadi ya fada wa jami'an soji cewa dole ne kwamanda ya nuna jarumtaka matukar yana son ya karfafa guiwar sojojinsa da sauran mayakan da ke karkashinsa. A ranar Jumma'a da ta gabata babban malamin shi'a a Iraqi Ayatollah Ali al-Sistani ya ce cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a cikin rundunar sojojin kasar dalili ke nan da ya sa mayakan IS suka samu galabar kwace wasu yankunan kasar.