An kwantar da Hosni Mubarak asibiti
April 13, 2011Wata kotu a ƙasar Masar ta bada umarnin cafke tsofan shugaban ƙasa Hosni Mubarak, bisa zargin rabda ciki da dukiyar ƙasa.Wannan umurni ya zo kwana ɗaya bayan da aka kwantar da tsofan shugaban a asibiti.
Dubunnan jam´a masu neman cenji su ka sake shirya zanga-zanga inda su ka buƙaci komitin soja da ke riƙwan ƙwarya a Masar ya bincike Mubarak da muƙƙarrabansa
Bayan zargin sama da faɗi, kotu na zarin Mubarak da aikata kisan gilla ga masu zanga-zangar neman cenji.
Wannan bincike da kotu ta ƙaddamar ya shafi Hosni Mubarak da ´ya´yansa guda biyu, Gamal da Alaa, da kuma wasu ministocin gwamnatinsa.
A wani bayani da ya yi a gidan talbajan na Alarabiya, Hosni Mubarack ya mussanta dukan zargin da ake yi masa, wanda ya dangata da makirci, domin zubda masa mutunci.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Zainab Mohamed Abubakar