1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwantar da sarkin Saudiyya a asibiti

Salisou BoukariDecember 31, 2014

Rahotanni daga na cewa, an kwantar da sarki Abdullah na Saudi Arabiya a wani babban asibiti da ke birnin Ryad, inda zai fuskanci wani binciken lafiya.

https://p.dw.com/p/1EDdP
Hoto: Hassan Ammar/AFP/Getty Images

Wata sanarwa ce dai da fadar Sarkin ta fitar a wannan Laraba ta bayyana hakan, inda ta ce an kwantar da shi ne, a asibitin King Abdulaziz da ke babban birnin kasar. Sai dai kuma sanarwar ba ta bada wani karin bayani kan halin da Sarki Abdullah ya ke ciki ba. Dan shekaru 90 da haihuwa, Sarki Abdullah ya hau karagar mulkin kasar ta Saudi Arabiya a shekarar 2005 bayan rasuwar dan uwansa Sarki Fahad. A watan Nuwamba na 2012 an taba yi masa tiyata na tsawon awoyi 11 a wannan asibitin da ke birnin Ryad, wanda kuma kafin nan ma an yi masa aiki a shekarun 2011 da ma 2010 bisa wannan matsala da ke damunsa ta mara.