An nada sabon Directan IMF
September 28, 2007Talla
Hukumar bada lamuni ta mdd watau IMF a atakaice,ta sanar da sunan tsohon ministan kula da harkokin kudi na faransa Dominique Strauss-Kahn a matsayin sabon babban Directan gudanarwanta .Directocin zartarwa na hukumar ta IMF sun sanar dacewa tsohon ministan faransa zai karbi madafan iko daga wajen shugabanta na yanzu kuma dan kasar Spania ,Rodrigo de Rato daga ranar 1 ga watan Nuwamba.A halin da ake ciki yanzu haka dai Strauss-Kahn yayi alkawarin gaggauta aiwatar da sauye sauye da ake muradi a wannan hukuma ta IMF.