An naɗa sabuwar Firaminista a Senegal
September 1, 2013Shugaban ƙasar ta Senegal Macky Sall ya naɗa Aminata Toure a matsayin firaministar ƙasar. Wannan ya biyo bayan da shugaban ya sallami firaministan ƙasar Abdoul Mbye, masani a harkar banki, wanda aka naɗa a bara don ya shugabanci gwamnatin ƙasar. Da ma tun da farko kakakin shugaban ƙasar Senegal Abou Abel Thiam, wanda ya bada sanarwar ba tare da ƙarin haske bisa dalilin sauke firimiyan ba, amma ya ce nan bada jimawa ba sa'a naɗa sabuwar firiminista da gwamnati. Aminata Toure ta faɗa wa wani gidan radiyon ƙasar cewa, "shugaban ƙasa ya umarceni da na kafa gwamnati, bayan da ya sallami tsohuwar majalisar ministoci". Kafin naɗin ta dai Aminata Toure, ita ce ministar shari'a a ƙasar.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal