An nemi yanke hukuncin kisa ga wani ɗan adawan Saudiyya
March 27, 2013Masu gabatar da ƙara a ƙasar Saudiyya sun nemi a yanke hukuncin kisa ga malamin da ya jagorancin yi wa gwamnati bore tamkar wanda ke faruwa a sauran ƙasashen Larabawa. Sheikh Nimr-Al nimr wanda ake ganin mai tsattsauran ra'ayi ne da ya fito daga yan Shi'a marasa rinjaye a Saudiyya, ya bayyana kotu a yau Ltinin, wanda shine karon fargo da aka gan shi tun watan Julin bara da jami'an tsaro suka kama shi. Ƙasar Saudiyya wanda yanzu haka ke kan gaba a marawa yan tawayen Siriya don su kiraf da gwamnati, lawyoyin ta suka ce neman a yi wa gwamnati bore wanda Shehin ya yi, tamkar yaƙi da Allah ne, don haka kamata ya yi a yanke masa hukuncin kisa bisa tsarin sharin musulunci. Yan sanda da masu adawa da gwamnatin sun yi ta artabu a ƙasar Saudiyya, musamman a yankin da yan Shi'a suka fi ƙarfi. Boren ana yinsa ne tun kusan shekaru biyu da aka fara zanga-zanga neman kafa mulkin demokraɗiyya a ƙasashen larabawa.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Zainab Mohammed Abubakar