1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Burhan ya sha rantsuwar sabon shugaban kasa

Mohammad Nasiru Awal AH
August 21, 2019

Janar Burhan zai jagoranci majalisar mulki mai membobi 11 tsawon watanni 21 na farko, kafin ya mika ragama ga wani jagora na farar hula da zai cike ragowar watanni 18.

https://p.dw.com/p/3OHK8
Sudan Abdel Fattah al-Burhan, Chairman Transitional Military Council (TMC)
Hoto: Imago Images/Xinhua

An rantsar da babban janar din kasar Sudan a matsayin jagoran gwamantin hadaka ta soja da farar hula da za ta joranci kasar tsawon shekaru uku har zuwa lokacin gudanar da zabuka.

Kamfanin dillancin labarun kasar, SUNA, ya ce a wannan Laraba Janar Abdel-Fattah Burhan ya sha rantsuwar kama aiki a gaban babban alkalin kasar, Maulana Abbas Ali Babikir. Janar Burhan zai jagoranci majalisar mulki mai membobi 11 tsawon watanni 21 na farko, kafin ya mika ragama ga wani jagora na farar hula da zai cike ragowar watanni 18.

Burhan ya jagoranci majalisar mulkin soji da ta karbi iko bayan an hambarar da shugaban mulkin kama karya Omar al-Bashir a watan Afrilu bayan tsawon watanni na zanga-zangar adawa da mulkinsa na shekaru 30.

An kafa sabuwar majalisar mulkin karkashin wata yarjejeniyar raba madafun iko tsakanin sojojin kasar da masu zanga-zanga.