An rantsar da sabon shugaban kasar Angola
September 26, 2017Talla
Sabon shugaban dai ya samu wannan matsayi ne bayan da jam'iyyarsa ta MPLA da ke mulkin kasar tun daga shekara ta 1975 ta yi nasara a zaben majalisar dokokin kasar da ya gudana ranar 23 ga watan Augusta. Bikin rantsar da sabon shugaban wanda shi ne shugaba na uku na kasar ta Angola kuma janar na soja mai ritaya Lourenço, ya wakana ne tare da halartar tsohon shugaban kasar José Eduardo dos Santos, da kuma shugabannin kasashen waje da dama cikinsu har da na kasar Ruwanda Paul Kagame, da na Aquatoriyal Guinea Teodoro Obiang Nguema.