An rasa rayuka a Sudan
May 14, 2019Talla
Masu zanga-zanga biyar ne tare da wani babban jami'in soja mai mukamin manjo, aka tabbatar da mutuwarsu a Sudan din, lokacin wani taho mu gama da aka yi a shelkwatar rundunar sojan da ke birnin Khartoum a daren Litinin.
Rigimar dai ta kaure ne bayan yarjejeniyar da majalisar mulki ta soji ta cimma da kungiyoyin adawa, dangane da mulkin kasar bayan kifar da gwamnatin tsohon Shugaba al-Bashir.
Ba a dai kaiga tabbatar da bangaren da ya soma kai wa wani hari ba, amma rundunar sojin Sudan din ta zargi wani gungun da bai ji dadin nasarar da aka samu tattaunawar ba, da kai harin.
Sai dai masu zanga-zanga na cewa sojojin da ke goyon bayan tsohon shugaban ne suka aikata aikin.