An rusa majalisar dokokin Jamus
December 27, 2024Za a gudanar da zaben kafa sabuwar gwamnati a Jamus a ranar 23 ga watan Fabairun 2025 ne bayan rushewar gwamnatin Olaf Scholz a watan Nuwambar 2024. Da yake tabbatar da ranar da za a yi zaben, Shugaba Frank-Walter Steinmeier ya jadadda bukatar samar da yanayi mai kyau a bangaren siyasar Jamus, tare da yin kira da a gudanar da yakin neman zabe cikin lumana da mutunta juna.
Karin bayani: Jamus: Kuri'ar yankar kauna kan gwamantin Scholz
Gwamnatin hadakar Jamus ta kawancen jam'iyyu uku ta rushe ne sakamakon rikicin cikin gida kan yadda za a farfado da kasar mafi karfin tattalin arziki a Turai, kana harin da aka kai kasuwar Kirismeti a makon da ya gabata ya sake tado da zazzafar muhawara kan tsaro da kuma bakin haure a kasar. Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai cigaba da kasancewa shugaban riko har zuwa lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati, wanda hakan zai dauki wasu watanni bayan kamalla zabe.